Rundunar ƴan sandan Kano ta hana hawan Babbar Sallah

Durbar 750x430

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sake jaddada dokar hana duk wasu ayyukan hawan Dawakai a fadin jihar yayin gudanar da bukukuwan Sallah mai zuwa, bisa dalilan tsaro.

Wannan Sanarwar ta zo ne sa’o’i kadan bayan da Majalisar Masarautar Kano ta fitar da wata sanarwa a karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II, inda ta gayyaci shugabannin gargajiya da mahaya Dawakai domin halartar bukukuwan Sallah da ake gudanarwa duk shekara.

A cikin wata sanarwa da ta fitar yau Talata tare da hadin gwiwa da jami’an tsaro, rundunar ‘yan sandan ta taya al’ummar Musulmi masu bin doka da oda, gabanin gudanar da bukukuwan Sallah, tare da yin kira ga jama’a da su bi ka’idojin kare lafiyar jama’a.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa, biyo bayan sahihan bayanan sirri da kuma tantancewar da aka yi na tsaro, an haramta duk wani nau’in ayyukan hawan Dawakai a duk fadin jihar, matakin da aka sanar tun da farko a lokacin ƙaramar sallar da ta gabata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here