Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi watsi da ikirarin da ake yi na cewa an batar da bindigogi 3,907 a rumbun ajiyar makamanta, inda ta bayyana cewa zargin yaudara ne kuma ba gaskiya ba ne.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, hedkwatar rundunar ta amince da kalubalen da aka fuskanta a lokacin kwantar datarzomar jama’a, da suka hada da kashe jami’an ‘yan sanda, hare-hare kan rumbun makamai, da kuma sace makaman.
Labari mai alaƙa: Majalisar dattijai ta sanar da bacewar bindigogi sama da 3,900
Sai dai kuma ya jaddada cewa an yi kokarin kwato su da kuma kididdigar makaman da aka batar.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ACP Muyiwa Adejobi, “an yi duk kokarin da aka yi na gano makaman da aka sace, kuma tuni aka kwato da dama kuma an mayar da su rumbun ajiyar kayan yaki na rundunar.”
Ya kara da cewa, “Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana mamaki da matukar damuwa dangane da labarin da ake yadawa na cewa an batar da makamai 3,907 daga rundunar ‘yan sandan Najeriya.
“Wadannan zarge-zargen yaudara ne kuma ba daidai ba ne.