Rundunar ƴan Sanda ta tabbatar da mutuwar mutane 2 tare da jikkatar guda yayin harin ƴan bindiga a Kwara

Kwara map 750x430

Rundunar ƴan Sandan Jihar Kwara ta tabbatar da cewa mutane biyu sun mutu yayin da wani guda ya jikkata a harin da ƴan bindiga suka kai garin Eruku a karamar hukumar Ekiti ranar Talata.

Rahotanni sun nuna cewa akwai rashin tabbas kan manufar harin, inda wasu suka ce ƴan bindigar sun bude wuta yayin shigarsu garin, yayin da wasu suka ce aikin sace mutane ne na yau da kullum.

Bidiyo da suka yadu a kafafen sada zumunta sun nuna mazauna garin da fasinjoji masu tafiya da motoci suna gudu don neman tsaro bayan harbin da ƴan bindigar suka yi.

A cikin wata sanarwa, kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Toun Ejire–Adeyemi, ya tabbatar da cewa mutane biyu sun mutu yayin da wani memba na ƙungiyar masu sanya ido ya samu raunuka.

Sanarwar ta bayyana cewa, rundunar ƴan Sanda ta Jihar Kwara tana tabbatar da harin ƴan bindiga a garin Eruku wanda ya faru a kusan karfe 18:00 na ranar 18 ga Nuwamba, 2025.

Shugaban ƴan sandan da Baturen yan sanda Eruku da tawagarsa, tare da haɗin gwiwar masu sanya ido, sun gaggauta mayar da martani ga karar harbi daga gefen garin, wanda hakan ya sa ƴan bindigar suka tsere cikin daji.

Bayan bincike sosai a wurin, an samu Gawar Aderemi, wanda aka harbe shi har lahira a cikin Coci Kristi Apostolic, Oke Isegun, yayin da wani, Tunde Asaba Ajayi, wanda shi ma aka harbe, aka samu a cikin daji, sannan mai sanya ido, Segun Alaja, ya samu raunukan harbi aka kai shi Asibitin ECWA, Eruku, don samun magani.

Kwamishinan ƴan Sanda na Jihar, Adekimi Ojo, ya yaba da saurin martanin ƴan sanda da masu sanya ido, tare da tabbatar wa jama’a cewa hukumomin tsaro ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai an kawar da ƴan bindigar gaba ɗaya.

Rundunar ƴan sanda ta ce za a ci gaba da bayar da sabbin bayanai yayin da bincike ke gudana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here