Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa darussan Turanci da Lissafi za su ci gaba da kasancewa dole ga dukkan ɗalibai masu rubuta jarabawar kammala sakandare (O’level).
Wannan bayani na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktar sashen yada labarai da hulda da jama’a ta ma’aikatar ilimi ta tarayya, Folasade Boriowo, ta fitar a birnin Abuja ranar Lahadi.
Sanarwar ta bayyana cewa, hakan na da nufin gyara fahimtar da wasu ke da ita game da sabon tsarin da aka sanar kan sauƙaƙe sharuɗɗan karɓar ɗalibai a manyan makarantu.
Ministan ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, ya fayyace cewa wannan gyara bai cire wajabcin ɗalibai su yi rajista ko su rubuta darussan Turanci da Lissafi ba a jarabawar su ta O’level.
A cewar ministan, sabon tsarin ya ƙunshi yadda za a bai wa ɗalibai damar samun gurbin karatu cikin sauƙi da daidaito, ta yadda ba za a hana masu ƙwarewa damar shiga jami’a ba saboda rashin nasara a wasu darussa da ba su da alaƙa kai tsaye da fannin da suka zaɓa.
Haka kuma, tsarin ya bai wa jami’o’i damar karɓar ɗalibai zuwa wasu shirye-shiryen karatu inda ake iya samun rangwamen buƙatar nasara a Turanci ko Lissafi, amma har yanzu ana buƙatar duk ɗalibai su yi rajista da rubuta waɗannan darussa.
Alausa ya ce wannan mataki na cikin hangen nesa na gwamnatin tarayya wajen inganta damar samun ilimi, haɗin kai da bunƙasa ƙarfin ɗan Adam, tare da amincewa da basira daban-daban da ɗalibai ke da su.
Ya kuma shawarci ɗalibai, iyaye da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi su dogara ga sahihan hanyoyin sadarwa na hukuma wajen samun bayanai kan sabbin manufofin gwamnati domin guje wa ɓata fahimta.
NAN













































