Ruɗani a Majalisar Dattijan Najeriya kan zargin cushe a kasafin kuɗi

Godswill Akpabio, majalisar, dattijai, najeriya, zargin, cushe, kasafin, kuɗi
Hayaniya ta kaure a zauren Majalisar Dattijai yayin da sanatoci ke muhawara kan zargin cushe a cikin kasafin kuɗin ƙasar, wanda shugaban ƙungiyar sanatocin...

Hayaniya ta kaure a zauren Majalisar Dattijai yayin da sanatoci ke muhawara kan zargin cushe a cikin kasafin kuɗin ƙasar, wanda shugaban ƙungiyar sanatocin arewa, Abdul Ningi ya yi a wata tattaunawa da sashen Hausa na BBC.

Tun da farko shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar Sanata Olamilekan Adeola daga jihar Ogun ya gabatar da ƙorafi kan tattaunawar da Sanata Ningi ya yi.

Karin labari: Burtaniya ta haramtawa ‘yan Najeriya da ma’aikatan lafiya zuwa kasashen waje

Ya soki lamirin kalaman Sanata Ningi kan cewa ana amfani da kasafin kuɗi iri biyu a ƙasar.

Sanata Adeola ya ce wannan tamkar cin zarafi da kuma ƙazafi ne.

Ya bayyana cewa kalaman sanata Ningi ba gaskiya ba ne, kasancewar tun asali babu kuɗin da aka ware a wasu ma’aikatu a cikin kasafin kuɗin da majalisar ta amince da shi.

Karin labari: Gwamnatin Tinubu ta musanta coge a kasafin kuɗin ƙasar

Sai dai Sanata Adamu Aliero daga jihar Kebbi ya bukaci shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio ya yi adalci wajen jin tabakin Sanata Ningi kan kalamansa.

A lokacin da ya yi sa’ilin muhawarar, Sanata Abdul Ningi ya bayyana cewa an yi wa kalaman nasa mummunar fahimta da fassara ne.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here