Gwamnoni a karkashin jam’iyyar PDP sun umurci lauyoyi da su shigar da karar shugaban kasa gaban kotun koli domin kalubalantar ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers, kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
Ƙarar da za a shigar a kotun koli a wannan mako, za ta bayyana majalisar dokokin kasar a matsayin wanda ake tuhuma na biyu.
A ranar 18 ga watan Maris ne shugaban kasa Bola Tinubu ya ayyana dokar ta baci a jihar ta Kudu maso Kudu, saboda rikicin siyasa da barnata gidajen mai.
Shugaban ya dakatar da Siminalayi Fubara, gwamnan jihar; Ngozi Odu, mataimakiyarsa da dukkan ‘yan majalisar na tsawon watanni shida.
Tinubu ya kuma nada Ibok-Ete Ibas, a matsayin mai kula da jihar Rivers.
Karin karatu: Gwamnatin tarayya za ta binciki yadda Fursunoni suka fasa gidan yari a Kogi
A ranar Alhamis, majalisar dattawa da ta wakilai sun amince da bukatar Tinubu na dokar ta-baci.
Sai dai gwamnonin PDP sun sha alwashin kalubalantar dokar ta-bacin a gaban kotu a taron ta na ranar Laraba.
Gwamnonin PDPn da suka haɗar da na jihohin Bauchi, Adamawa, Bayelsa, Enugu, Osun, Plateau, da Zamfara ne suka fara gabatar da karar, inji TheCable.
Tuni dai bisa hukuncin da kotun koli ta kasar ta yanke a baya, Fubara bai iya samun damar shigar da karar ba saboda zai bukaci izini daga gwamnati mai ci a Rivers.
Gwamnonin suna bukatar kotu ta bayyana cewa bisa tanadin sashe na 1(2) da 5(2) da kuma na 305 na kundin tsarin mulkin Najeriya “Shugaban Najeriya ba shi da hurumin dakatar da zababben gwamna da mataimakin gwamna bisa tafarkin dimokuradiyya bisa fakewa ko kuma bin dokar ta-baci”.
Suna kuma fatan kotu ta bayyana cewa shugaban kasa ba shi da hurumin dakatar da zababbun yan majalisar dokoki ta jiha bisa ga sashe na 192 (4) (6) da na 305 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (kamar yadda aka gyara).
Karin karatu: Fursunoni 12 sun tsere daga gidan yari a jihar Kogi
Masu shigar da karar sun kuma bukaci kotun koli ta bayyana dakatar da Fubara, mataimakiyarsa da mambobin majalisar dokokin jihar Rivers “ba bisa ka’ida ba, sannan kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima).”
Babu tabbas ko gwamnonin suna da hurumin shigar da karar saboda babu daya daga cikinsu da dokar ta-baci ta shafa.
Sai dai masu bincike sun ce sun kuduri aniyar gwada dokar “domin gaba”.