Rikicin ranar Idi: Sufeto janar na ƴan sandan Najeriya ya janye gayyatar da ya yiwa Sarki Sanusi

Muhammad Sanusi II

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta janye gayyatar da ta yi wa Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II a baya dangane da wani rikici da ya faru a jihar Kano yayin bikin Sallah a ranar 30 ga Maris, 2025.

Tun da farko dai an yi wannan gayyata ne domin baiwa Sarki Sanusi damar ba da bahasi kan abubuwan da suka haifar da ketare doka da oda da aka sanya na hana Hawan sallah a jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ranar Lahadi.

“Biyo bayan shawarwarin masu ruwa da tsaki da ake mutuntawa tare da yin daidai da kudurin Sufeto-Janar na ‘yan sanda na tabbatar da cewa ba a siyasantar da ayyukan ‘yan sanda ba ko kuma a yi musu mummunar fassara ba, IGP ya ba da umarnin a janye gayyatar,” in ji sanarwar.

‘’Maimakon haka, an umurci jami’an hukumar leken asiri ta Force Intelligence Department (FID) bisa umarnin IGP da su wuce Kano domin samun bayanin daga Sariki Sanusi.

“Kafin ranar sallah an samu rahoton yadda sarakunan biyu a Kano ke kokarin yin Hawan sallah domin ganawa da jama’ar su, wanda hakan ya sanya muka aike da jami’ai da kuma bada shawarar hana yin Hawan don samar da zaman lafiya”.

‘’Duk da wannan yarjejeniya, Alhaji Sanusi wanda ya halarci Sallar Idi a cikin motarsa, ya yanke shawarar hawan doki ne bayan Sallar Idi a ranar Sallah tare da rakiyar ’yan banga, hakan ya haifar da wata arangama da matasan unguwar suka yi, wanda ya yi sanadin mutuwar wani matashi Usman Sagiru, tare da jikkata wasu da dama”.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here