An bukaci babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja da ta kori sabon mai rikon muƙamin shugabancin jihar Rivers Vice Admiral Ibokette Ibas, mai ritaya.
Cikin karar an bayyana shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda ake tuhuma na 1, sai babban Lauyan tarayya da kuma Vice Admiral Ibas mai ritaya da kuma Atoni-Janar na jihohi 36 da birnin tarayya, an lissafa su a matsayin wadanda ake tuhuma na 2 zuwa na 39 a cikin karar mai lamba: FHC/ABJ/CS/572/2025 a gaban kotu ranar Talata.
Karar wanda wani lauyan mazaunin Abuja, Mista Johnmary Jideobi ya shigar, yana kuma rokon kotun da ta yi watsi da duk wani mataki da yanke hukunci na wanda ake kara na 3 Admiral Ibokette Ibas mai ritaya daga amsa sunan shugaban riko na Rivers da sauran bukatu.
A cewar mai shigar da kara, ya shigar da wannan kara ne domin amfanin jama’a, domin kare Doka da kuma tabbatar da makomar kundin tsarin mulki da kuma kiyaye mutuncin kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda shi ne kundi mafi karfi da ke rike da Jihar Najeriya cikin daidaito da kuma zama.
Karanta: Ba a cika sharuɗɗan da ake buƙata ba wajen yiwa Natasha kiranye – INEC
A halin yanzu dai, ba a sanya ranar da za a saurari wannan batu ba.