Yunkurin tsige gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa Ngozi Odu ya sake fuskantar cikas bayan wasu ƙarin mambobi biyu na Majalisar Dokokin Jihar sun janye goyon bayansu ga wannan mataki.
Ƴan majalisar sun yi kira da a nemi mafita ta hanyar sulhu domin warware rikicin siyasar da ke addabar jihar.
Barile Nwakoh, mai wakiltar mazabar Khana ta ɗaya, da Emilia Amadi, mai wakiltar mazabar Obio/Akpor ta biyu, sun bayyana matsayinsu ne bayan awanni 48 kacal da wasu ƴan majalisa biyu suka sanar da irin wannan matsaya.
Ko da yake sun amince cewa ana zargin gwamnan da mataimakiyarsa da karya wasu tanade-tanaden kundin tsarin mulki, sai dai sun ce sauya matsayinsu ya biyo bayan shiga tsakani daga manyan shugabanni da masu ruwa da tsaki da suka nemi a yi haƙuri domin kare zaman lafiya da daidaito a Jihar Rivers.
Karanta: Da ɗumi-ɗumi: Majalisar dokokin Rivers ta fara shirin tsige Gwamna Fubara
Da wannan sabon sauyi, yanzu mutum huɗu daga cikin ƴan majalisa 26 da suka fara amincewa da sanarwar zargin aikata manyan laifuka sun nisanta kansu daga yunkurin tsige gwamnan, lamarin da ke nuna ƙara ƙarfi na kiran tattaunawa maimakon rikici a cikin majalisar.
Ana sa ran Majalisar Dokokin Jihar Rivers za ta sake zama domin zaman majalisa a ranar 15 ga watan Janairu, 2026, yayin da hankula suka karkata kan yadda shugabancin majalisar zai tafiyar da rikicin ra’ayoyi da ke ƙara tsananta.
Tun da fari, shugaban marasa rinjaye na majalisar, Sylvanus Nwankwo, mai wakiltar mazabar Omuma, da Peter Abbey na mazabar Degema, sun riga sun sanar da janyewarsu daga shirin tsige gwamnan, inda suka bukaci a nemo hanyoyin warware rikicin siyasar domin kauce wa dagula tafiyar da mulki a jihar.












































