Rikici ya ɓarke a jam’iyyar NNPP tsakanin Ɗan majalisar tarayya da Mai magana da yawun gwamnan Kano

WhatsApp Image 2025 06 10 at 18.45.07 750x430

Rikici ya ɓarke a jam’iyyar jam’iyyar NNPP a jihar Kano yayin da ɗan majalisar tarayya Tijjani Abdulkadir Jobe, mai wakiltar mazabar Dawakin Tofa, Tofa, da Rimin Gado, ya fito fili ya soki Sanusi Bature Dawakin Tofa, Babban Daraktan yaɗa Labarai na Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf kan soyayyar siyasarsa da iyalan tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa a cikin wani faifan bidiyo da aka yi a karshen mako, Jobe ya yi kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya gargadi mai magana da yawunsa, Sunusi Bature, kan zargin alakarsa da iyalan Ganduje a Dawakin Tofa.

Ya bayyana dangantakar a matsayin barazana ga hadin kai da nasarar jam’iyyar NNPP a jihar.

“Ina kira ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, idan za ka ci gaba da aiki da Sunusi Bature a matsayin kakakin ka, kuma ya dawo nan Dawakin Tofa don kulla kawance da Abba Ganduje, don Ganduje, da Gwaggo Matar Ganduje to dole a magance wannan,” in ji Jobe.

Ya kara da cewa, “Idan da gaske Sunusi Bature dan jam’iyyar NNPP ne, to ya daina sa ‘yan jam’iyyar su na yabon Abba Ganduje.

Rikicin siyasar ya kara tsananta ne bayan Sunusi Bature ya mayar da martani ga kalaman Jobe ta shafinsa na Facebook da aka tabbatar, wanda ke nuni da fara fito na fito da jama’a.

Bature ya kuma jaddada mahimmancin bin diddigi a tsakanin zababbun jami’an, inda ya ce kamata ya yi shugabanci ya dogara ne da hidima, ba son rai ba.

” Girmamawa da nake yi masa ya ta’allaka ne akan aikin da ya yi na yiwa mutanen da suka zabe shi aiki, hakkinsu na hannun sa na kariya da kuma kiyayewa, duk wanda aka zaba ya wakilce mu dole ne ya cika hakkin jama’a,” in ji shi.

Dan majalisar a baya dan jam’iyyar APC ne kafin ya koma jam’iyyar NNPP gabanin zaɓen shekarar 2023.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here