Majalisar Musulmi ta Jihar Bauchi ta bayyana cikakken goyon baya ga Sanata Shehu Buba Umar, Shugaban Kwamitin Tsaro da Leken Asiri na Majalisar Dattawa, bisa ƙoƙarinsa na magance matsalar tsaro ta hanyar tattaunawa da sulhu.
A taron manema labarai da aka gudanar a ofishin ƙungiyar yan jarida NUJ a Bauchi, shugaban majalisar, Injiniya Ahmad Yusuf, ya ce tsari da dabarun Sanata Buba suna nuna ƙwazo da kishin zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasa.
Ya bayyana cewa majalisar, wacce ke ƙarƙashin inuwar ƙungiyoyin Musulmi a jihar, tana da niyyar ƙarfafa haɗin kai, gyaran ɗabi’a, da haɗa kai da gwamnati da ƙungiyoyin farar hula domin tabbatar da adalci, zaman lafiya da kyakkyawan shugabanci.
Yusuf ya jaddada cewa rikice-rikice tsakanin makiyaya da manoma, gasa ta siyasa, rikicin al’umma, sabanin addini, tayar da hankalin matasa, da tasirin sauyin yanayi na daga cikin abubuwan da suka jawo rashin tsaro a ƙasar nan.
Ya bayyana cewa ƙoƙarin Sanata Buba na haɗa tattaunawa da tsare-tsaren tsaro na gwamnati ya riga ya haifar da sakamako a Bauchi ta Kudu.
Karin labari: Likitoci sun dakatar da yajin aikin gargaɗi da suka fara
A cewarsa, tattaunawa tsakanin manoma da makiyaya ta rage rikice-rikice, kasuwanni sun sake buɗewa, kuma an fara dawo da amincewa tsakanin maƙwabta.
Haka kuma, ƙungiyoyin sa ido na cikin al’umma da aka kafa karkashin jagorancinsa suna ba hukumomin tsaro bayanai, lamarin da ya sanya jama’a suna shiga cikin shirin zaman lafiya maimakon kasancewa a matsayin waɗanda rikici ke ci gaba da cutarwa.
Majalisar ta yi Allah wadai da yaɗa jita-jita da sukar da ake yi wa Sanata Buba, tana mai cewa kasancewarsa a kujerar shugabanci mai muhimmanci ba zai taɓa yin abin da zai tauye tsaron ƙasa ba.
Majalisar ta kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kula da waɗanda rikici da ƙauracewa muhallansu suka rutsa da su, tare da roƙon malamai da ‘yan siyasa su guji maganganu masu zafi da siyasantar da batun tsaro.
A ƙarshe, Majalisar Musulmi ta Bauchi ta sake nanata aniyarta na ci gaba da tallafawa zaman lafiya, tattaunawa da sulhu, a daidai da manufarta ta ƙarfafa haɗin kai tsakanin Musulmi da tabbatar da daidaito a cikin al’ummar Najeriya baki ɗaya.













































