Rashin Tsaro: El-Rufai ya zargi gwamnatin Tinubu da ƙarfafa ayyukan ƴan bindiga

el rufai Speaking

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya zargi gwamnatin tarayya da ƙarfafa ayyukan ƴan bindiga da ke addabar sassan kasar.

Ya yi zargin cewa gwamnati na ba ‘yan bindiga karfi ta hanyar biyansu alawus alawus na wata-wata, ta aika musu da abinci, yana mai bayyana hakan a matsayin manufar kusanto da ƴan bindigar.

“Abin da ba zan yi ba shi ne in biya ‘yan bindiga alawus-alawus, ko aika musu da abinci da sunan wadanda ba su da hannu a ciki. Wannan maganar banza ce; muna ba ‘yan bindiga karfi ne kawai”.

A hirar sa da gidan talabijin na Channels, tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja Elrufa’i ya ce “Ba gwamnatin jihar Kaduna ba ce faruwar al’amuran rashin tsaro, manufar kasa ce da ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro kuma Kaduna na cikinta. Janyo ƴan bingidar a jiki wannan ita ce sabuwar manufar,”.

Ya caccaki abin da ya bayyana a matsayin manufar inganta ƴan bindiga maimakon mayar da martani ga laifukan da suka aikata.

Wannan a cewarsa shi ne ya haddasa matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a kasar.

Tsohon gwamnan da ya yi wa’adi biyu ya bayyana cewa, “A koyaushe matsayata ita ce ƴan bindigar da suka tuba matattu ne kawai, mu kashe su duka, mu jefa musu bam har sai sun zama babu komai, sannan kashi biyar din da ake son a gyara su za a iya gyara su.

Ana ci gaba da nuna damuwa kan rashin tsaro a kasar nan, musamman a yankin Arewa, inda a baya-bayan nan aka kai hare-hare a jihohin Katsina, Benue, da Filato.

Duk da cewa har yanzu gwamnatin tarayya ba ta mayar da martani ga ikirarin El-Rufai ba, sai dai mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, a watan Yuli ya bayyana cewa hare-haren Boko Haram, da ‘yan fashi da kuma rikicin kabilanci a yankin Arewa ya ragu matuka a cikin shekaru biyu na gwamnatin shugaba Bola Tinubu, idan aka kwatanta da yadda al’amura suke a gwamnatin baya.

A wani misali, hukumar ta NSA ta bayyana cewa an kashe mutane 1,192 tare da yin garkuwa da sama da 3,348 a jihar Kaduna a zamanin gwamnatin da ta gabata, yayin da sama da mutane 5,000 suka rasa rayukansu a jihar Benue a cikin wannan lokaci.

Da take ba da misali, NSA ta ce an kashe mutane 1,192 tare da yin garkuwa da sama da 3,348 a jihar Kaduna a zamanin gwamnatin da ta gabata, yayin da aka kashe sama da 5,000 a jihar Benue a cikin wannan lokaci.

Rundunar sojin Najeriya ta tura dakaru 197 Gambia don bada gudunmawar tsaro

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga shugabannin Arewa a taron tattaunawa na kwanaki biyu da gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya a jihar Kaduna.

Ribadu ya ce nasarorin da aka samu a yaki da rashin tsaro sun biyo bayan umarnin da shugaba Tinubu ya bayar ga hukumomin tsaro kan tsarin tsaron bai daya.

Ya ce ayyukan tsaro daban-daban da aka gudanar a yankin Arewa maso Yamma ya sa aka sako mutane 11,259 da aka yi garkuwa da su a watan Mayun 2025.

Ya kuma bayyana cewa jami’an tsaro sun kawar da shugabannin ‘yan fashi da dama da ‘yan kungiyarsu a jihohin Zamfara, Kaduna, da Katsina.

Hakazalika, a watan Afrilu, NSA ta bukaci ‘yan Najeriya da su daina baiwa masu garkuwa da mutane kudaden fansa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here