Hukumar ɗa’ar ma’aikatan shari’a ta jihar Kogi ta bayar da umarnin dakatar da wani alkalin kotun yankin, Alemeru Adekunle Bamidele, ritayar dole bisa rashin ɗa’a.
Hukumar ta kuma dakatar da Alkali Tanimu U. Muhammed daga aikin shari’a na tsawon shekaru biyu tare da ba shi takardar gargadi.
An yanke wadannan hukunce-hukuncen ne a taron JSC na 136 da aka gudanar a Lokoja, kamar yadda wata sanarwa da sakataren hukumar, Dr. Tanko Muhammed ya fitar ranar Alhamis.
Sai dai hukumar ta wanke wasu mutane hudu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban. Su ne Alkalin Kotun, Abdul Musa Mopah, Yunusa Medugu, Deborah O. Ebiloma Esq. da Anuhi Safiya Oiza.
Karin karatu: Tinubu ya nemi majalisar dattawa ta tabbatar da shugabanni da mambobin hukumar gudanarwar NCDC
Sakataren hukumar, Dakta Tanko Muhammed, wanda ya yi magana kan hukuncin da hukumar ta yanke ranar Alhamis a Lokoja, ya kuma ce hukumar ta kafa wani kwamiti mai mutum shida domin duba yiwuwar inganta jin dadin alkalan kotunan yankin.
Kwamitin a cewarsa yana karkashin jagorancin babban mai shari’a kuma kwamishinan shari’a na jihar Muizudeen Abdullah.