Shugaban ƙasar Iran Masoud Pezeshkian tare da wasu manyan jami’ai biyu za su jagoranci ƙasar a lokacin rikon ƙwarya bayan mutuwar jagoran koli Ali Khamenei, kamar yadda talabijin na ƙasa ya ruwaito a ranar Lahadi.
Shugaban ɓangaren shari’a Gholamhossein Mohseni Ejei da kuma wani jami’i daga majalisar kula da harkokin doka za su kasance cikin mutum uku da za su sa ido kan tafiyar da mulki a lokacin sauyin, inda kafar ta ambato Mohammad Mokhber, ɗaya daga cikin masu ba Khamenei shawara.
Amurka da Isra’ila sun ƙaddamar da hare-hare kan wasu wurare a Iran a ranar Asabar, lamarin da ya haifar da martanin gaggawa daga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da mutuwar Ali Khamenei, inda talabijin na ƙasar Iran ya tabbatar da labarin da safiyar Lahadi.
Mutuwar Khamenei ta haifar da tambayoyi masu muhimmanci kan makomar ƙasar.
A tsarin mulkin Iran, wata majalisar malamai mai mambobi 88 da ake kira Majalisar Kwararru ce ke da alhakin zaɓen sabon jagoran koli, kuma tana da ikon tsige shi, ko da yake hakan bai taɓa faruwa ba.
Karin karatu: Iran ta ayyana zaman makoki na kwanaki 40 bayan rasuwar Khamenei
Dokar Iran ta tanadi cewa dole ne majalisar ta zaɓi sabon jagora cikin gaggawa, amma kafin hakan, kwamitin rikon ƙwarya zai iya karɓar dukkan ayyukan jagoranci na wucin gadi.
Idan hakan ya faru yanzu, Shugaba Masoud Pezeshkian da shugaban ɓangaren shari’a Gholamhossein Mohseni Ejei za su kasance cikin wannan kwamitin.
Ana kuma ganin ɗan Khamenei mai suna Mojtaba a matsayin mai yiwuwa ya gaje shi, duk da cewa bai taɓa riƙe wani muƙamin gwamnati ba.
Sauyin mulki irin wannan ya taɓa faruwa sau ɗaya ne kacal a shekarar 1989 bayan rasuwar Ayatollah Ruhollah Khomeini.
Jagoran koli na Iran na da cikakken iko kan harkokin ƙasa, shi ne babban kwamandan sojoji da rundunar kare juyin juya hali, kuma yana da ikon yanke hukunci kan manyan batutuwan siyasa da tsaro a ƙasar.













































