PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Kano

PDP PDP 750x430

Jam’iyyar PDP a jihar Kano, ta yi watsi da sakamakon zaɓen mazaɓar Bagwai/Shanono da Ghari/Tsanyawa da aka sake gudanarwa, saboda maguɗi da tashin hankali da ta ce an yi a zaben.

Jam’iyyar ta yi ikirarin cewa ‘yan daba ne suka tada hatsaniya yayin zaben, inda ‘yan barandan siyasa suka riƙa tsoratar da wadanda suka je kaɗa ƙuri’a, lamarin da ya mayar da zaɓen tamkar wasa.

Shugaban jam’iyyar, Alhaji Yusuf Kibiya, wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a ranar Asabar a Kano, ya bayyana tsarin a matsayin wanda “babu dukkanin tsarin dimokradiyya”.

Ya kuma yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta INEC da ta samar da daidaito ga dukkan jam’iyyu, ya na mai jaddada cewa halin da ake ciki a yanzu ya na kawo cikas ga sahihancin gudanar da zaben.

Ya yi kira ga jami’an tsaro da su kare masu kada kuri’a, su tabbatar da gudanar da zabe cikin lumana, tare da dakile cin zarafi da tashin hankali.

Shugaban ya shawarci gwamnatin jihar Kano da shuwagabannin kasa da su guji zage-zage da cin mutunci, sannan ya bukace su da su inganta tsarin zabe na gaskiya da kwanciyar hankali.

Ya kuma yi kira ga hukumomin da abun ya shafa da su binciki saba dokokin zabe tare da sanya takunkumi ga masu laifi don hana aikata ba daidai ba a nan gaba.

Rundunar ‘yan sanda a ranar Asabar din ta sanar da kama wasu matasa 288 da ake zargin ‘yan daba ne a yayin sake zaben mazabar Ghari/Tsanyawa da kuma Bagwai/Shanono.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Ibrahim Bakori ne ya bayyana hakan ga manema labarai a karamar hukumar Shanono.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here