Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta sake ɗage babban taronta na ƙasa NEC, wanda yanzu aka mayar ranar 15 ga Mayun 2025.
Jam’iyyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar, wadda babban sakatarenta, Sunday Ude-Okoye ya sanya wa hannu.
Karin karatu: Atiku yayi watsi da rahotannin sauya sheka Daga jam’iyyar sa ta PDP
Tun da fari jam’iyyar ta sanar da babban taron ta ne a ranar 13 ga Maris, sannan aka ɗage saboda wasu zaɓukan cike gurbi da aka yi a wasu jihohi da yankuna.
Tun a shekarar da ta gabata ce dai aka saka ranar babban taron na 98, amma ana ɗagewa, wanda wataƙila hakan bai rasa nasaba da wasu matsaloli da jam’iyyar ke fuskanta.