Ofishin Jakadancin Amurka ya gargaɗi ƴan ƙasar su guji zuwa sansanin soji da ofisoshin gwamnati

IMG 20250623 WA0036

Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar da sanarwar tsaro ya na mai shawartar ‘yan Amurkan da su guji tafiye-tafiye marasa mahimmanci zuwa cibiyoyin soji da na gwamnati a Abuja saboda karuwar matsalar tsaro a duniya.

Ta cikin sanarwar da Ofishin Jakadancin Amurka ya fitar a yau Litinin ya bayyana cewa, a halin yanzu an haramta wa duk ma’aikatan ofishin jakadancin da iyalansu ziyartar wuraren soji ko wasu wuraren gwamnati da ke babban birnin tarayya, sai dai in da wata manufa ta hukuma.

Wannan shawarar ta zo ne sakamakon ci gaban da ba a fayyace ba a duniya wanda ya haifar da tsauraran matakan tsaro da kuma sake nazarin motsi a wurare masu mahimmanci.

An yi kira ga ‘yan kasar Amurka da ke zaune a Najeriya ko masu ziyara da su kasance cikin taka-tsan-tsan a wuraren taruwar jama’a, musamman a wuraren da Turawan Yamma da ‘yan kasashen waje, da kuma jami’an gwamnati ke zuwa.

Har ila yau, ofishin jakadancin ya ba da shawarar guje wa manyan taruka da kiyaye al’amuran da ba za a iya tantancewa ba, da kuma sanin hanyoyin ficewar gaggawa a cikin gine-gine.

Ana karfafa gwiwar ‘yan kasar Amurka da su sake duba tsare-tsarensu na tsaro da kuma yin taka-tsantsan yayin zamansu a Najeriya.

Sanarwar ta kara da cewa, “Saboda karuwar matsalar tsaro da ke tasowa daga abubuwan da ke faruwa a duniya a halin yanzu, Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya sanar da ‘yan kasar Amurka cewa duk ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka da iyalansu an hana su yin balaguron da ba na hukuma ba zuwa wani wurin sojan Najeriya ko wani wurin gwamnati da ke Abuja a wannan lokaci.

Duk da sabbin takunkumin, Sassan karamin ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja da karamin ofishin jakadancin da ke Legas na nan a bude kuma suna aiki.

An shawarci jama’ar da ke neman ƙarin bayani ko neman taimako da su ziyarci shafin Internet na ofishin jakadancin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here