NNPP ta buƙaci INEC ta sanya Tambarin jam’iyyar na asali a takardun zaɓe

NNPP

Lauyan jam’iyyar NNPP, Mista Ndubuisi Ukpai esq, ya rubuta wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, wasika, inda ya bukaci hukumar ta dakatar da duk wani zabe har sai an sanya sahihin tambarin jam’iyyar a jikin takardun zabe na gaba.

Hakan na kunshe ne a cikin wasikar da jam’iyyar ta raba wa manema labarai yau Laraba a birnin Lagos.

Wasikar, mai kwanan ranar 25 ga watan Agusta, kuma aka ta aika zuwa ga shugaban INEC, mai take: “RE: SUIT NO.: CV/3210/2025; New Nigeria Peoples Party VS Independent National Electoral Commission: Ci gaba da wakilcin sahihin shugabancin jam’iyyar NNPP da bukatar ci gaban jam’iyyar, Ta bayyana cewa ya kamata INEC ta guji gudanar da duk wani zabe har sai ta sanya tambarin jam’iyyar NNPP na gaskiya da adalci da kuma shigar jam’iyyar karkashin jagorancin Dr Major Agbo a matsayin shugabanta na kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here