Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta bayyana cewa za a samu ruwan sama tare da ƙaƙƙarfar iska a sassa daban-daban na ƙasar nan daga Litinin zuwa Laraba.
A cikin hasashen yanayi na kwanaki uku da aka fitar a ranar Lahadi a Abuja, hukumar ta ce a ranar Litinin da safe za a samu guguwar iska da ruwan sama matsakaici a jihohin Arewa da suka haɗa da Sokoto, Zamfara, Kebbi, Katsina, Kaduna, Kano, Bauchi, Gombe da Taraba.
Hukumar ta ƙara da cewa daga baya cikin rana, za a samu guguwar iska tare da ruwan sama a wasu sassa na Kebbi, Zamfara, Sokoto, Kaduna da Taraba.
A shiyyar tsakiyar ƙasa, NiMet ta bayyana cewa za a samu yanayi mai ɗan gajeren hadari da hasken rana a wasu lokuta, tare da guguwar iska da ruwan sama a wasu jihohi kamar Niger, Kwara, Babban Birnin Tarayya (Abuja), Kogi, Benue da Nasarawa. Daga bisani kuma, za a samu ruwan sama matsakaici a wasu daga cikin waɗannan jihohi.
Haka kuma, a shiyyar kudu, hukumar ta ce za a samu yanayi mai ɗan gajeren hadari tare da ruwan sama kaɗan a wasu jihohi kamar Oyo, Ogun, Legas da Cross River da safe. Daga baya cikin rana, an hasashen guguwar iska tare da ruwan sama matsakaici a faɗin shiyyar.
Karin labari: Gwamnan Bauchi ya kori Kwamishina a cikin ƙaramin sauyin da zai samar a majalisar zartarwa
NiMet ta kuma yi gargadin yiwuwar ambaliya a jihohin Benue, Taraba da Cross River, inda ta shawarci al’ummar wuraren da abin ya shafa su fara ɗaukar matakan gaggawa don guje wa illa.
Hukumar ta bayar da shawarwari da suka haɗa da: gudu yayin tuƙi lokacin ruwan sama, kauce wa wuraren da ake samun ambaliya, da kuma guje wa amfani da takin zamani ko maganin kwari kafin ruwan sama.
Haka zalika, an shawarci jama’a su tabbatar sun daure abubuwan waje da za su iya haura iska, su cire na’urorin lantarki yayin guguwar iska da kuma nisantar manyan bishiyoyi don guje wa haɗarin rassan da ka iya faɗowa.
Hukumar ta kuma bukaci kamfanonin jiragen sama da su riƙa karɓar rahoton yanayi na filayen jiragen sama kafin shirin tashi ko saukar jirage.
NiMet ta ƙara da shawartar jama’a da su riƙa bibiyar shafin ta na internet www.nimet.gov.ng da sauran kafafen hukuma don samun sahihan bayanai game da yanayi domin kiyaye lafiyar su da dukiyoyin su.













































