Nijar ta karɓi baƙuncin tawagar Iran

Ali, Mahaman, Lamine, Zeine, Nijar, Iran, bakunci, tawagar
A jiya ne Firaministan Nijar, Ali Mahaman Lamine Zeine ya karbi baƙuncin tawagar Iran ƙarƙashin jagorancin mataimakin ministan harkokin tattalin arziki na...

A jiya ne Firaministan Nijar, Ali Mahaman Lamine Zeine ya karbi baƙuncin tawagar Iran ƙarƙashin jagorancin mataimakin ministan harkokin tattalin arziki na Iran, Mehdi Safari a ma’aikatar harkokin wajen ƙasar.

Gidan talabijin na ƙasar Tele Sahel ya rawaito cewa tattaunawar ta kasance kan aiwatar da jerin kwangiloli da zasu amfani ɓangarorin biyu.

Karin labari: Kwastam za ta rabawa jama’a kayan abincin da ta kwace

“Mun shirya yin hadin gwiwa da Nijar a fannin ɗanyen mai da matatun mai da tashoshi da kuma ma’ajiyarsu” in ji Safari.

Nijar na sake fasalin manufofinta na ketare, inda ta ƙara kusantar ƙasar Rasha bayan takun saka tsakaninta da Faransa da sauran kawayenta na yamma kan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here