NELFUND: BUK, Kwalejin Kimiyya ta Kano, Jami’ar Ilorin da sauran makarantu 200 sun gaza mika bayanan ɗalibai don neman tallafin karatu (Jadawalin sunayen)

NELFUND 750x430

Asusun bada tallafin karatu ga Dalibai na Ilimi a Najeriya (NELFUND) ya fitar da jerin sunayen manyan makarantu 203 da suka kasa ɗora bayanan ɗalibansu a tsarin neman tallafin karatu na shekarar 2024/2025.

Asusun ya kuma sanar da sake buɗe shafin internet din sa na tsawon sa’o’i 48 domin bai wa waɗanda ba su cika wannan buƙata ba damar yin hakan kafin lokacin ƙarshe.

Rahoton SolaceBase ya bayyana cewa an umarci dukkan jami’o’i, kwalejoji da cibiyoyi na gaba da sakandare su shigar da bayanan ɗalibansu a cikin tsarin neman tallafin dalibai (SLAS), wanda ke ba ɗalibai damar neman rancen ilimi ta hanyar hukumar.

Labari mai alaƙa: NELFUND ta sake buɗe shafin bada launin ɗalibai na shekarar karatu ta 2024/2025

A cikin sanarwar da Daraktar Sadarwa ta dabaru na hukumar, Oseyemi Oluwatuyi, ta fitar a ranar Juma’a da daddare, ta bayyana cewa shafin internet zai kasance a buɗe daga ƙarfe 12 na dare ranar Lahadi, 12 ga Oktoba, zuwa ƙarfe 12 na dare ranar Talata, 14 ga Oktoba, 2025.

Cikin jerin cibiyoyin da suka gaza mika bayanan ɗalibai akwai Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Kwalejin Fasaha da Kimiyya ta Kano, Jami’ar Ilorin, Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, Jami’ar Ibadan, Jami’ar Abuja, da kuma wasu jami’o’i da kwalejoji daga jihohin Najeriya daban-daban da suka haɗa da Osun, Kaduna, Jigawa, Katsina, Kwara, da Taraba.

Asusun NELFUND ya gargadi cewa duk wata makaranta da ta kasa kammala shigar da bayanan ɗalibanta a cikin lokacin da aka ƙayyade za ta rasa damar shiga cikin zagayen tallafin karatu na bana, abin da zai iya cutar da ɗaliban da za su amfana da tsarin.

Hukumar ta kuma bayyana cewa domin tabbatar da gaskiya da bayyananniyar hanya, za ta fitar da cikakken jerin sunayen makarantu da suka gaza bin umarnin.

NELFUND ta jaddada aniyarta ta tabbatar da daidaito da adalci wajen samar da damar samun ilimi ga kowane ɗalibi ta hanyar gudanar da tsarin tallafin karatu cikin gaskiya da inganci.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here