NDLEA ta hada hannu da ƙungiyar Yan Dambe domin yakar shaye-shaye a Kano

NDLEA Kano 750x430

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA shiyyar Kano ta ce, za ta haɗa hannu da ƙungiyar ƴan Damben Gargajiya ta Mazaje Traditional Sport Promotion Limited domin yakar shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Sadiq Muhammad-Maigatari ya fitar yau Asabar a Kano.

Sanarwar ta ce, ɗaukar matakin na daga cikin tattaunawar da bangarorin biyu suka yi a lokacin da Sarkin Damben Gargajiya na Najeriya, Bashir Muhammad-Danliti ya jagoranci tawagar sa suka kai ziyarar ban girma ga hukumar NDLEA a Kano.

Ganawar wadda ta kasance wani ɓangare na ayyukan da aka shirya gabanin ranar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Majalisar Dinkin Duniya, wadda ake yi a kowace shekara a duk ranar 26 ga watan Yuni.

A nasa ɓangaren, Kwamandan hukumar ta NDLEA na Kano Abubakar Idris Ahmad, ya bayyana cewa, sun yi hadin guiwar ne da nufin yin amfani da wasannin gargajiya musamman ma Dambe domin jawo hankalin matasa da wayar da kansu kan illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi da safarar kayan maye.

Idris Ahmad wanda ya samu wakilcin shugabar sashen daƙile amfani da miyagun ƙwayoyi ta hukumar Hajiya Maimuna Garba, ta bayyana jin dadin ta ga kungiyar ta Mazaje bisa irin goyon bayan da ta ke bayarwa wajen yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Haka kuma, ta yaba wa jami’in kula da harkokin wasanni Jamilu Uba Adamu, bisa sabbin hanyoyin da ya bi wajen samar da wasanni a matsayin dandalin yada muhimman sakonni kan wayar da kan jama’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here