Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA sun cafke wani tsohon dan wasan kwallon kafa na duniya, Segun George Hunkarin, tare da wani abokin kasuwancinsa Ntoruka Emmanuel Chinedu, bisa kokarin fasa kwaurin hodar iblis zuwa Najeriya ta filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja a jihar Legas.
SolaceBase ta ruwaito cewa, Chinedu, wanda ya kasance babban mai safara ta jirage da ya shahara wajen jigilar kaya daga Turkiyya zuwa Najeriya da suka hadar da situru da kayan abinci, shi ne na farko da aka kama lokacin da ya isa filin jirgin saman Lagos a ranar Talata, 24 ga watan Yunin bana.
A wani bincike da aka yi a cikin jakarsa an gano cewa, ya boye wasu kunshi na hodar iblis guda 37 masu nauyin gram 800 a ciki.
Wata sanarwa da daraktan yada labarai na hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a yau Lahadi, ta ce bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya fito ne daga kasar Turkiyya ta jirgin Ethiopian Airlines, amma ya wuce birnin Addis Ababa na kasar Habasha, inda ya karbo kayan daga hannun wani mutum kafin ya nufo Najeriya.
Haka kuma, ya ce, binciken da aka yi ya nuna cewa wani abokin huldarsa wanda ya zama tsohon kwararren dan wasan kwallon kafa, Segun Hunkarin, ya na jiran Chinedu a wurin ajiye motoci na filin jirgin sama domin ya karbar masa kaya.

Hunkarin, wanda ya dau shekaru a Brazil ya na taka leda a kungiyoyin kwallon kafa, ba tare da bata lokaci ba aka kama shi a wurin ajiye motoci.
A cikin bayaninsa, Hunkarin ya yi ikirarin cewa a lokacin da ya ke buga wasan kwallon kafa a kasar Brazil wadda ke yankin Kudancin Amurka, ya taba yin safarar miyagun kwayoyi sau biyu daga Brazil zuwa Habasha, amma bai taba kawowa Najeriya ba ko sau daya.
A ranar Juma’a 27 ga watan Yuni ne jami’an NDLEA suka kama wani dan kasuwa a nahiyar Turai mai suna Amen Okoro Godstime a filin jirgin sama na Lagos a lokacin da ya ke yunkurin safarar kwayoyin Tramadol 225mg guda 5,000 da aka kunshe cikin magungunan zazzabin cizon sauro kamar Lonart, Amatem da Aluktem zuwa kasar Spain.
An kama shi ne a dakin tashi na tasha ta 2 na filin jirgin sama yayin da fasinjoji ke shirin hawa jirgin Royal Air Maroc da zai nufi Spain ta Casablanca.
Okoro, wanda ke sana’ar jigilar kayayyaki da tsakanin kasashen Turai da Najeriya, ya yi ikirarin cewa idan ya isa kasar Spain zai hau jirgin kasa zuwa kasar Faransa, inda ya ke zaune, daga nan kuma ya aika da tramadol din zuwa kasar Italiya domin yin cinikinta.












































