NDLEA ta ba da shawarar a tilasta yin gwajin miyagun ƙwayoyi ga masu neman lasisin tuƙa mota

WhatsApp Image 2024 09 05 at 14.51.14 750x430

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta ba da shawarar a saka gwajin ingancin miyagun ƙwayoyi a matsayin tilas ga duk masu neman lasisin tuƙi a ƙasar nan.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa wannan shiri na daga cikin matakan da ake ɗauka domin rage yawaitar haɗuran mota da ake samu sakamakon tuƙi a lokacin maye a sassan ƙasar nan.

Shugaban NDLEA, Janar Buba Marwa (Rtd.), ya bayyana haka a sakon godiya da ya aike wa taron ƙasa na Ƙungiyar shuagabanni na Musamman na hukumar kiyaye abkuwar haɗɗura (FRSC) da aka gudanar ranar Laraba a birnin Abuja, ta hannun mataimakinsa, Umoru Ambrose, inda ya bayyana cewa FRSC da NDLEA abokan haɗin gwiwa ne wajen kare rayukan jama’a.

Marwa ya bayyana cewa bincike ya nuna amfani da miyagun ƙwayoyi yana taka muhimmiyar rawa wajen haddasa haɗura a kan hanyoyi.

Ya ce saboda haka ne aka shiga haɗin gwiwa da FRSC, tare da shirya yarjejeniyar fahimtar juna wadda ke dab da kammaluwa domin amfanin jama’a.

Ya ƙara da cewa yarjejeniyar za ta baiwa jami’an FRSC damar yin gwajin miyagun ƙwayoyi nan take ga direbobi a hanya.

Karanta: Tinubu ya bada umarnin karɓo bashin Naira biliyan 30 da ake bin dillalan kayan noma

A cewarsa, wannan mataki zai zama kariya ga fasinjoji da kuma duk wani abin tsoro ga direbobin da ke sha ko amfani da miyagun ƙwayoyi yayin tuƙi.

Shugaban NDLEA ya bayyana cewa an riga an horar da kwararru da za su koyar da jami’an FRSC yadda ake yin gwajin nan take, tare da cewa hukumar za ta fara aiwatar da shirin a kan tituna da zarar komai ya kammala.

A nata jawabi, Mataimakiyar Kwamanda Janar ta FRSC, Pauline Olaye, ta yaba da wannan shawara, tana mai cewa taron Marshal na Musamman na bana wata dama ce ta nazari, tsara sabbin dabaru da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa wajen inganta tsaro a kan hanyoyin ƙasar.

Ta ce sadaukarwa da jajircewar Marshal na Musamman wajen aikin sa-kai ya dade yana taka muhimmiyar rawa wajen ceto rayuka da tabbatar da bin doka a kan tituna.

Ta bayyana jigon taron na bana da taken “Matsayin Marshal na Musamman a Harkar Tsaron Hanyoyi” a matsayin mai dacewa da yanayin zamani da buƙatar ƙarin haɗin kai.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here