NBC ta dakatar da Eedris Abdulkareem daga yaɗa wakarsa ta “Tell Your Papa” a gidajen rediyo da Talabijin

eedris abdulkareem Tinubu 750x430

Hukumar kula da kafafen yada labarai ta Kasa ta haramtawa gidajen rediyo da Talabijin na Najeriya su yaɗa wakar nan mai taken “Tell Your Papa” ta fitaccen mawakin nan, Eeedris Abdulkareem, inda ta yi nuni da cewa “abin kyama ce.”

A cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan watan Afrilu 9, 2025 kuma mai kula da harkokin yada labarai, Susan Obi ta fitar, ta ce hukumar ta ayyana wakar a matsayin abar ƙin yadawa a karkashin sashe na 3.1.8 na dokar yada labarai ta Najeriya.

Wannan sashe ya hana watsa abubuwan da ake ganin bai dace ba, zagi, ko keta mutuncin jama’a musamman a kafafen watsa labarai na kasa.

A cewar NBC, yayin da waƙar ta sami ƙarfi a dandalin sada zumunta, abubuwan da ke cikin waƙar sun kasa cika ka’idojin yadawa.

Wakar dai mai cike da cece-kuce da aka fitar a farkon makon nan, ta shafi Seyi Tinubu, ɗan shugaban kasa Bola Tinubu, inda ta yi kira gare shi da ya tunkari mahaifinsa kan tabarbarewar yanayin zamantakewa da tattalin arziki a Najeriya.

A cikin waƙar mai taken “Ka Faɗa wa Babanka,” wanda aka watsa a X (Twitter) a ranar Lahadi, Abdulkareem ya gabatar da wani sako inda ya zana hoton wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta na yau da kullum.

Wakar ta zo ne a matsayin martani ga kalaman Seyi Tinubu a kwanan baya a jihar Adamawa, inda ya bayyana mahaifinsa a matsayin “babban shugaban kasa a tarihin Najeriya.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here