NBA da hukumar kula da sadarwa NCC sun horar da Lauyoyi kan kare haƙƙin mallaka a Kano

WhatsApp Image 2025 09 08 at 17.50.05 750x430

Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen Ungogo a Kano tare da haɗin gwiwar hukumar sadarwa ta ƙasa NCC sun gudanar da taron horaswa na yini guda domin ba da ƙwarewa ga lauyoyi kan kare haƙƙin mallaka da sauran al’amuran da suka shafi shi.

Taron ya ja hankalin lauyoyi da dama, inda aka gabatar da laccoci kan batutuwa kamar su fahimtar haƙƙin mallaka da haƙƙoƙin da ke da alaƙa da shi a Najeriya, iyakoki da ke akwai a tsarin doka, laifuffuka da magance su, da kuma ƙalubale da damar da ke cikin amfani da Internet.

Shugaban NBA reshen Ungogo, Ahmad Abubakar Gwadabe, ya ce an shirya taron ne domin ƙarfafa membobin ƙungiyar da fahimtar yadda ake kare haƙƙin mallaka musamman wajen magance matsalolin satar fasaha da karya doka.

Ya bayyana cewa lauyoyi na bukatar sanin haƙƙoƙi da hane-hane a karkashin dokar haƙƙin mallaka domin kare abokan huldarsu yadda ya dace.

Karin karatu: Ba zaki dawo aiki yanzu ba – Majalisar dattawa ta faɗawa Natasha

Shi ma mai rikon mukamin kwamishinan NCC a Kano, Sani Ahmad, ya bayyana taron a matsayin wani ɓangare na dabarun hukumar wajen yaki da satar fasaha da kuma wayar da kai kan sabbin tanade-tanaden dokar haƙƙin mallaka da aka gyara kwanan nan.

Ya ce hukumar ta ɗauki matakin rashin sassauci kan masu aikata sata, tare da gudanar da sintiri, wayar da kai, da kuma kwace kayayyakin da aka sata.

Duka NBA da NCC sun bayyana jin daɗinsu da yadda taron ya gudana, tare da jaddada cewa haɗin gwiwa mai ɗorewa zai taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa tsarin kare haƙƙin mallaka a Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here