Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA) ta sanar da shirin dawo da karɓar kuɗin haraji na $300 daga masu jiragen sama masu saukar ungulu a fadin ƙasar.
Da yake jawabi a taron shekara-shekara na 53 na Ƙungiyar Masu Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Najeriya a ranar Alhamis a Jihar Kano, Daraktan Sashen Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama na NAMA, Tayo John, ya bayyana ƙalubalen kuɗi da hukumar ke fuskanta da kuma buƙatar dawo da wannan kuɗin.
Yayin gabatar da takarda mai taken “Matsalolin Kuɗi da Suka Shafi Ba da Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama a Najeriya: Tasiri da Matakan Magancewa,” John ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta umarci hukumar da ta dakatar da karɓar kuɗin a baya, amma yanzu sun shirya dawo da shi.
“Nan da makonni kaɗan za mu sake fara karɓar kuɗin saukar jirgin sama na $300 daga masu jiragen sama masu saukar ungulu,” in ji John.
“Mun fara tun da farko, amma gwamnati ta umarci mu dakatar saboda wasu matsaloli a ƙasar. Amma a wannan karon, ba za mu ƙara jan kafa ba.”
Duk da cewa ba a bayyana takamaiman ranar da za a fara aiwatar da wannan kuɗin ba, John ya jaddada cewa wannan matakin yana da mahimmanci domin rage matsalolin kuɗi da hukumar ke fuskanta.