Gwamnatin Najeriya ta miƙa ragamar harkokin cibiyar wutar lantarki na Zungeru zuwa ga wani kamfani mai zaman kansa na Penstock Limited.
An bayyana haka ne a taron farko na hukumar NCP da ke tantance kadarorin gwamnati da suka kamata a sayar a bana da aka yi a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Karanta wannan: MDD ta ƙaƙaba takunkumi kan jagororin ‘ƴan tawayen Kongo
Ana sa rai matakin zai inganta harkar samar da wutar lantarki tare da bayar da gudummawa sosai ga biyan buƙatun ‘ƴan ƙasa game da makamashi.
An cimma yarjejeniyar ranar 13 ga watan Disambar 2023 tsakanin hukumar kula da kadarorin gwamnati BPE da kamfanin na Penstock Limited.
Bayan amincewar hukumar NCP, kamfanin ya amince ya biya kashi hamsin cikin 100 na kuɗin soma aiki ranar 5 ga watan Janairu.
Karanta wannan: NiMet ta yi hasashen samun jinkirin saukar ruwan sama a bana
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima wanda ya jagoranci taron ya bayyana ƙudurin gwamnatin tarayya na sake fasalta bankin tallafawa ayyukan noma domin haɓaka ɓangaren noma da samar da abinci a ƙasa.
Da yake magana a taron, Shettima ya bayyana irin rawar da bankin zai taka wajen samar da abinci a ƙasa inda ya yi magana kan rassan bankin da ke yankunan Najeriya.