Najeriya Ta Fi Kowace Ƙasa Arhar Wutar Lantarki a Duniya – Gwamnatin Tarayya 

download
download

Ministan wuta na ƙasa, Abubakar Aliyu a jiya laraba ya bayyana cewa kuɗin da ake amsa na wutar lantarki a Najeriya ya fi na ko ina arha a duniya.

Ya kuma ce duk da wannan garaɓasar da wutar ta ke da ita da kuma irin ƙoƙarin da gwamnati ta ke yi na ganin wutar ta wadaci ‘yan Najeriya, mutane da dama ciki harda wasu manyan ma’aikatun gwamnati ba sa son biyan kuɗin wutar.

Ministan ya dai yi wannan jawabi ne jiya a Abuja a yayin wata tattaunawa da kwamitin wuta na majalisar dattawa, tare da kuma shuwagabannin wasu ɓangarori na hukumomin wutar lantarkin kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Ya ƙara da cewar a Najeriya ana siyar da ma’aunin kilowat na wutar ne akan $0.15 na dalar Amurka, wanda ya yi daidai da N105. A jamhuriyar Nijar kuwa $0.42 ne na dala, $0.23 a Benin, $0.25 a Mali, $0.28 a Senegal, sai kuma $0.27 a Burkina Faso.

Da ya ke jawabi, manajan daraktan TRCN, wato hukumar rarraba wuta ta ƙasa, Sulaiman Abdulaziz yace rashin biyan kuɗin wutar da manyan ma’aikatun gwamnati su kan yi ne ya janyo aka ɗage wutar da ake bawa kamfanonin KAEDCO na Kaduna da KEDCO na Kano daga ma’aikatar wuta ta ƙasa a kwanakin baya. Ya ƙara da cewar duk da dai yanzu an mayar da su na wucin gadi, dole ne ya zamto an biya kuɗin wutar ga hukumar rarraba wutar ta ƙasa a cikin kwanaki 60 da aka ba su dama.

Sai dai a na shi ɓangaren, shugaban kwamitin majalisar na ɓangaren wuta Sanata Gabriel Suswam, da kuma wasu daga cikin mambobin kwamitin irin su Sanata Adamu Aliero da Yusuf sun bada shawarar cewa kamata ya yi ma’aikatar kuɗi ta ƙasa ta riƙa cirewa daga asusun ma’aikatun da suka ƙi biyan kuɗin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here