Tsohon babban Hafsan tsaron ƙasa, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa Najeriya ƙasa ce da ta cancanci a tsaya a kare ta, inda ya buƙaci sojoji su ci gaba da jajircewa wajen kare tsaron ƙasa da mutuncin al’umma.
Ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a birnin Abuja, yayin bikin ban kwana na musamman da aka shirya masa bayan kammala aikin soja na tsawon shekaru 39.
Janar Musa ya yi tunani kan rayuwarsa ta soja, inda ya bayyana hidimarsa ga ƙasa a matsayin babbar girmamawa da ya samu a rayuwarsa.
Ya ce bikin da aka gudanar a yau ba wai al’ada ce kawai ba, illa dai wata alama ce ta ƙarshen wani dogon tafiya da ya sadaukar domin kare ƙasar da tabbatar da haɗin kan al’umma.
Janar Musa ya bayyana godiya ta musamman ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya naɗa shi a matsayin babban hafsan tsaro a shekarar 2023, saboda amincewa da amana da kuma damar da ya ba shi wajen yi wa ƙasa hidima.
Haka kuma, ya gode wa sauran manyan hafsoshin tsaro da al’ummar Najeriya bisa goyon bayansu da haɗin kan da suka bayar wajen tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar.
Yayin da yake bankwana da rigar sojarsa, Janar Musa ya miƙa gaisuwa ta musamman ga iyalinsa, matarsa da ‘ya’yansa bisa jimirin da suka yi yayin dogon zaman sa a bakin aiki da kuma damuwar da suka fuskanta.
Ya buƙaci jami’an rundunar tsaro su ci gaba da aiki da sadaukarwa, gaskiya, da ƙwarewa kamar yadda ya yi a tsawon aikinsa, yana mai jaddada cewa nasarorin da rundunar soji ke samu ba na ɗan lokaci ba ne, illa na dogon lokaci ne idan aka ci gaba da haɗin kai.
Janar Musa ya kuma yi kira ga ƙarin haɗin kai tsakanin rundunonin tsaro na ƙasar, yana mai cewa babu wata hukuma ɗaya da za ta iya lashe yaƙin tsaro ita kaɗai.
Ya yaba wa rundunar ‘yan sanda, hukumar leƙen asiri ta ƙasa (DSS), hukumar bayanan sirri ta Najeriya (NIA), da sauran hukumomin tsaro bisa gudunmawar da suka bayar a tsawon shekaru.
Ya kuma gode wa al’ummar Najeriya, musamman matasa, bisa addu’o’insu da kwarin gwiwar da suke nunawa wajen ganin an samu makoma mai kyau ga ƙasar, yana mai cewa hakan shi ne ginshiƙin ƙoƙarin rundunar soji.
Ya ce, “Ina nan a matsayin soja a zuciya, ɗan ƙasa mai kishin kare ikon Najeriya. Ko da wannan ne ƙarshen aikin soja na, zan ci gaba da yin hidima ga ƙasa ta ta kowace hanya da zan iya.”
NAN













































