NAHCON ta sanar da sabon farashin kuɗin aikin Hajjin 2026

NAHCON Chairman Prof Abdullahi Saleh Usman sabo 750x430

Hukumar kula da aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da sabon kuɗin aikin Hajjin shekarar 2026 bayan umarnin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayar na rage farashin.

Wannan sanarwa ta fito ne ranar 26 ga watan Satumba.

Sanarwar ta bayyana cewa umarnin na zuwa ne daga Tinubu, ta hannun mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima yayin ganawar da ya yi da shugabannin hukumar NAHCON ranar Litinin, 6 ga watan Oktoba.

Shettima ya bayyana cewa rage kuɗin aikin hajjin ya zama wajibi saboda darajar Naira na ci gaba da ƙaruwa idan aka kwatanta da Dalar Amurka, wanda shi ne babban abin da ke shafar farashin tafiyar.

Hukumar NAHCON ta bayyana cewa sabon farashin aikin hiajjin na shekarar 2026 wanda aka ƙayyade bayan tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa, ya nuna ragin Naira dubu dari biyu idan aka kwatanta da kuɗin da aka biya a shekarar 2025 a dukkan yankuna na ƙasar.

Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ce maniyyata daga yankin Maiduguri/Yola wanda ya haɗa jihohin Adamawa, Borno, Taraba da Yobe, za su biya Naira 8,118,333.67 a shekarar 2025, amma yanzu za su biya Naira 7,579,020.96.

Haka kuma, maniyyata daga sauran yankunan Arewacin za su biya Naira 7,696,769.76 maimakon Naira 8,244,813.67 da aka biya a bara, yayin da masu tafiya daga kudancin ƙasa za su biya Naira 7,991,141.76 maimakon Naira 8,561,013.67 da suka biya a shekarar da ta gabata.

Usman ya ƙara da cewa an tsayar da ranar Juma’a, 5 ga watan Disamba a matsayin ranar ƙarshe ga masu niyyar biyan sabon kuɗin aikin Hajjin, domin tabbatar da cikakken shiri da bin umarnin shugaban ƙasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here