Shugaban jam’iyyar (APC) na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da su guji duk wani abu ko magana da ka iya haifar da rabuwar kai a cikin jam’iyyar.
Alhaji Abbas ya yi wannan gargadi ne a matsayin martani ga muhawarar da ke gudana kan tabbatar da nadin injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin shugaban hukumar da ke kula da harkokin lantarki ta ƙasa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar da kansa a daren ranar Juma’a, shugaban jam’iyyar ya nuna damuwa cewa wannan rikici na iya janyo rarrabuwa tsakanin mambobin jam’iyyar da kungiyoyin goyon bayansu a jihar.
Labari mai alaƙa: Dalilin da ya sa muka dakatar da tantaceGarba Ramat a matsayin shugaban NERC – Majalisar Dattawa
Ya bayyana cewa kalaman da wasu magoya bayan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, da na wadanda ke tare da dan takarar gwamna da mataimakinsa na jam’iyyar APC, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna da Hon. Murtala Sule Garo, na iya kawo cikas ga haɗin kan jam’iyyar.
Ya kara da cewa wannan batu na cikin nauyin kundin tsarin mulki na fadar shugaban ƙasa da majalisar dattawa, inda fadar shugaban ƙasa ke da hurumin tsayar da sunan wanda za a nada, yayin da majalisar ke da ikon tantancewa da tabbatarwa bisa tanadin doka.
Alhaji Abbas ya tunatar da mambobin jam’iyyar cewa duk da bambance-bambancen ra’ayoyi da ake samu a siyasa, jam’iyyar APC ta kasance ɗaya kuma haɗaɗɗiya tun daga farko.
Ya roƙi mambobin jam’iyyar da su yi hattara kada su bari sabani kan nadin mutum ɗaya ya rushe zumuncin da ya dade yana haɗa su, tare da yin kira ga kowa da kowa da ya mutunta tsarin doka, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin tarayya da majalisar dokoki za su gudanar da al’amarin yadda ya dace domin amfanin ƙasa da jam’iyya.













































