Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Najeriya, Joe Ajaero ya ce sun fito zanga-zanga ne a yanzu ganin cewa idan suka jinkirta yinta, mutane da dama za su iya mutuwa saboda tsananin halin matsi da jama’a ke ciki sakamakon tsadar rayuwa.
Ajaero ya bayyana haka ne a yau yayin da ƙungiyar ke zanga-zangar yini biyu a faɗin Najeriya domin bayyana rashin jin daɗinta game da yanayin da ƙasar ke ciki.
Karin labari: ‘Ƴan ƙwadago sun kutsa cikin majalisar dokokin Najeriya
A hirarsa da manema labarai a dandalin zanga-zangar a Abuja, ya ce shugabannin Najeriya sun tabbatar da yadda mutane suka shiga garari sakamakon matsin rayuwa sai dai a cewarsa, abin da gwamnati ke cewa a kullum shi ne a ba ta lokaci.
“Shi ne muke cewa idan aka ci gaba da haƙuri, to kowa na iya mutuwa kafin lokacin da za’a yi wani abu, ku yi wani abu yanzu, shi ne kawai banbanci.” in ji shi.
Karin labari: Tinubu ya gana da hamshaƙan ‘ƴan kasuwar Najeriya
“Muna duba lokacin, muna son a yi wani abu cikin gaggawa kafin wata shekarar, dole mutane su rayu kafin su ci gajiyar aikin” kamar yadda ya ce.
Ajaero ya ce yana da yaƙini cewa shugaba Tinubu zai yi wani abu game da halin da jama’a ke ciki.
Shugaban na NLC ya ce babu wani ma’aikaci da zai rayu kan mafi ƙanƙantar albashi na naira dubu talatin inda ya ce fiye da ‘ƴan Najeriya miliyan ɗari da hamsin ba su ƙetara layin fatara ba wato a cewarsa, ba sa iya samun abin kaiwa baka a kullum.