Ministan harkokin cikin gida, Dokta Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana duba buƙatun samun zama ƴan ƙasa daga mutum 170 da suka fito daga ƙasashen waje.
Ministan ha bayyana hakan ne ta shafinsa na X, wanda a da ake kira Twitter, inda ya ce kwamitin bada shawara kan batun zama ɗan ƙasa ne ke nazari da kuma ba da shawarar waɗanda shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu zai amince da su.
Tunji-Ojo ya ce wannan aiki gwaji ne ga amincin shugabanni, kuma za su tabbatar da gaskiya da amana wajen aiwatar da shi.
Ya ƙara da cewa zama ɗan ƙasa a babbar ƙasa bakar fata mafi girma a duniya babbar dama ce da ke buƙatar kulawa da la’akari sosai.
Ministan ya bayyana cewa kwamitin ya ƙunshi manyan jami’an gwamnati daga ma’aikatar shari’a, ma’aikatar harkokin waje, hukumar tsaro ta farin kaya, da kuma hukumar shige da fice ta ƙasa.
A cewarsa, gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu za ta ci gaba da aiki tukuru domin bunƙasa ƙasar tare da mayar da ita wuri mai jan hankalin mutane daga ko’ina cikin duniya.
NAN













































