Ba sabon labari ba ne cewa an saki ƴan matan nan biyar waɗanda masu garkuwa da mutane suka sace a Abuja.
Masu garkuwa da mutane sun sace ƴanmatan guda shida da mahaifinsu ne a gidansu da ke Abuja.
Daga baya suka saki mahaifin yaran mai suna Mansour Al-Kadriyah tare da umartarsa da ya je ya nemi naira miliyan 60 kafin a saki yaran.
Sai dai bayan mako ɗaya, mahaifin yaran bai samu damar biyan kuɗin ba, inda masu garkuwan suka kashe ɗaya daga cikin yaransa mai suna Nabeeha, wadda ba ta daɗe da kammala karatun jami’a ba, sun yi hakan ne a matsayin gargaɗi ga iyayen domin su gaggauta nemo kuɗin fansa.
Karanta wannan: Kamaru ta zama kasar farko da ta kaddamar da gangamin rigakafin cizon sauro
Haka nan ma a wannan lokacin sun ƙara yawan kuɗin fansar da suke nema.
Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama suka fara bayar da gudunmawar kuɗi ga iyalan domin a ceto ƴan matan.
An saki ƴan matan ne bayan shafe kwana 19 a hannun masu garkuwa da mutane.
A ranar Talata da dare, mai magana da yawun ƴan sandan Najeriya reshen tarayyar Abuja, Josephine Adeh, ta sanar da cewa jami’an ƴan sanda sun kuɓutar da ƴan matan.
Karanta wannan: Dalilin da yasa digirin bogi ya zama ruwan dare a Najeriya – NUC
Wata sanarwa da Adeh ta fitar, ta ce ƴansanda tare da haɗin gwiwar jami’an sojin Najeriya ne suka samu nasarar ceto yaran.
Sai dai, lokacin da BBC ta tuntuɓi iyalan Al-Kadriyah don jin yadda aka saki ƴanmatan, abun da suka faɗa ya saɓa da na ƴansanda da kuma sojoji.
Kawun yaran, Sheriff Al-Kadriyah, wanda malami ne a sashen addini da tarihi na Jami’ar Jihar Kwara, ya bayyana cewa su suka kuɓutar da yaransu.
Sheriff ya ce sun biya kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutanen kafin a saki ƴanmatan.
Ya ce bayan biyan kuɗin da kwanaki huɗu ne masu garkuwar suka kira su da su zo su karɓi yaran a jihar Neja.
Karanta wannan: Majalisar Dattawa za ta gayyaci Wike kan karuwar satar mutane – Kingibe
“Ƴan uwa ne a cikin iyalai suka haɗu domin biyan kuɗin fansar da kuma fitar da iyalin cikin wahalar da suka shiga.”
“Ba zan iya faɗan nawa muka biya masu garkuwa da mutanen ba domin sakin ƴanmatan saboda dalilai na tsaro, amma sun karɓi maƙudan kudaɗe a hannunmu.”
Ya ce da gaske ne sojoji sun raka waɗanda suka kai kuɗin domin kare su.
“Ba gaskiya ba ne cewa ƴansanda ne suka ceto ƴanmatan ba, mun biya kuɗin fansa kafin sakin su.
Karanta wannan: Mutane uku sun rasu a jihar Nasarawa sakamakon zaftarewar kasa
Sheriff Al-Kadriyah ya gode wa dukkan waɗanda suka taimaka musu da tallafin kuɗi domin sakin ƴaransu, inda ya ce kuɗin ya taimaka musu sosai wajen ceto yaran nasu.
Ya ƙara da cewa bayan shafe kwanaki 19 a hannun masu garkuwa da mutane, akwai buƙatar duba lafiyar yaran.
Ya ce ƴan matan suna asibiti a yanzu inda ake ci gaba da kula da su.
Karanta wannan: ‘Yan sanda sun ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi a hanyar Abuja
Ya kuma ce mahaifin yaran shi ma yana asibiti, inda yake samun kulawa saboda masu garkuwa da mutanen sun jikkata shi kafin su sake shi ya je ya nemi kuɗi.
Sheriff Al-Kadriyah ya kuma bayyana cewa a ranar da masu garkuwa da mutanen suka miƙa gawar Nabeeha, akwai wasu gawawwaki 3 na mutanen da aka kashe.