MTN ya bai wa ƴan Najeriya haƙuri kan ƙarin kuɗin kira da na data

MTN 3

Kamfanin sadarwa na MTN a Najeriya ya bai wa masu amfani da layukansa haƙauri kan ƙarin kuɗin kira da na data da kamfanin ya yi a ƴan kwanakin nan.

A farkon makon nan ne aka wayi gari da ƙarin kusan kashi 200 cikin ɗari, lamarin da ƴan ƙasar da dama suka yi Allah wadai da shi.

To sai dai cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a shafinsa na X, ya ce yana sane da yadda masu amfani da layukansa suka nuna damuwa bayan da suka wayi gari kwatsam da ganin ƙarin kusan kashi 200 na kuɗin data.

Kamfanin ya ce zai iya bayar da dalilan da suka sa ya ɗauki matakin ƙarin, to sai dai ya ce in ma ya yi hakan ba zai gamsar ba.

Labari mai alaƙa: Ƙungiyar ƙwadago ta buƙaci ƴan Najeriya su ƙaurace wa kamfanonin sadarwa

“Saboda da haka mun karɓi laifinmu, mun yi kuskure, muna bayar da haƙuri kan hakan, a kuma yafe mana” a cewar kamfanin.

Ƙarin dai ya tayar da ƙura a Najeriya, lamarin da ya sa ƙungiyar ƙwadago NLC ta buƙaci al’umma su ƙaurace wa amfani da layukan manyan kamfanonin wayar daga ƙarfe 11 na safe zuwa 2:00 na rana a kullum daga yau Alhamis, 13 ga watan Fabarairu har zuwa 28 ga watan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here