Mazauna Zaria sun nemi ɗauki bayan ambaliya ta lalata Maƙabarta da makarantu

images 5 6

Mazauna garin Chikaji da ke karamar hukumar Sabon-Gari a jihar Kaduna, sun buƙaci gwamnati da masu hannu da shuni da su kawo musu dauki, sakamakon ambaliyar ruwa.

Ambaliyar ruwan ta mamaye maƙabarta da gidaje da dukiyoyi a yankin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito.

Ambaliyar wadda ta mamaye yankin a ranar Litinin, ta biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka kwashe sa’o’i bakwai ana yi tun daga karfe 5:00 na Asuba zuwa karfe 1:00 na rana.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Talata a Zariya, Hakimin kauyen Chikaji, Alhaji Auwal Sani-Dambaba, ya ce, ambaliyar ta shafi gidaje sama da 200 a yankin.

Ya kara da cewa ambaliyar ruwan ta yi awon gaba da wasu sassa na makarantar firamare tare da lalata wani muhimmin bangare na makabartar Ojo.

“A halin yanzu, wadanda abin ya shafa sun fake a unguwar, amma ba a samu asarar rai ba yayin faruwar lamarin.

Duk da haka, an bar kaburbura da yawa a bude,” in ji shugaban kauyen.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here