Allah Ya yi wa fitaccen mawaƙin Hausa a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, El-mu’az Muhammad Birniwa, ya rasu.
Kafin rasuwar haziƙin mawaƙin ya yi waƙoƙi da dama, kuma ɗan asalin ƙaramar hukumar Birniwa ne ta jihar Jigawa, an haife shi a jihar Kaduna inda a nan ya taso, ya gudanar da rayuwarsa.
Muna addu’ar Allah ya gafarta masa.