Matar Tinubu ta kai wa Aisha Buhari ziyara fadar shugaban ƙasa

345432715 2484807461668585 7874444566067574950 n
345432715 2484807461668585 7874444566067574950 n

Matar shugaban Najeriya Aisha Buhari ta zagaya – da matar zaɓaɓɓen shugaban ƙasar mai jiran rantsuwa Sanata Oluremi Tinubu – don nuna mata lungu da saƙon gidan da shugaban ƙasar ke zama tare da iyalansa.

Aisha Buhari ta ce gidan da a yanzu iyalan shugaban ƙasar ke zaune a ciki da ake yi wa laƙabi da ‘Glass House’ a fadar shugaban ƙasar Villa, shi ne gidan da shugaban ƙasar mai barin gado da iyalansa za su zauna gabanin sauka daga mulki.

Ta ƙara da cewa gidan ‘Glass House’ shi ne muhallin da shugaban ƙasa mai barin gado zai koma domin bayar da damar yi wa ainihin gidan shugaban ƙasar mai jiran-gado kwaskwarima.

A nata ɓangare uwargidan shugaban ƙasar mai jiran gado Sanata Oluremi Tinubu ta yaba wa Aisha Buhari bisa tarbar da ta yi mata, inda ta alƙawarta yin aiki tuƙuru domin ci gaban al’ummar ƙasar.

A ranar 29 ga watan Mayu ne za a rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin sabon shugaban ƙasar da zai maye gurbin Muhammadu Buhari wanda ke kammala wa’adin mulkinsa na biyu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here