Wata mata mai shekara 39 wadda ake zargin ta kashe mahaifiyarta ta hanyar ɗirka mata maganin hawan jini fiye da ƙa’ida ta miƙa kanta ga ƴansanda.
Lamarin ya faru ne a ranar 12 ga watan Yuni, inda matar ta kai kanta ga ofishin ƴansanda a garin Bengaluru na ƙasar Indiya.
A lokacin da ta isa ofishin, matar mai suna Sonali Sen, ta shaida wa ƴansanda cewa ita ce ta kashe mahaifiyarta da kanta.
Ta kuma ce mahaifiyar tata ce ta umurce ta da yin hakan.
A lokacin da ta yi ƙarin bayani kan lamarin, Sonali ta ce bayan ta kashe mahaifiyar tata, ta sanya gawar a cikin akwati kafin daga bisani ta ɗauko ta ta tunkaro ofishin ƴan sanda.
A lokacin da suka duba, ƴan sanda sun gano hoton mahaifin Sonali a cikin akwatin gawar, wanda ya daɗe da rasuwa.
Ƴansanda sun ce Sonali ta banka wa tsohuwar tata ƙwayoyin magani hawan jini har guda 30, inda bayan wani ɗan lokaci ta samu bugun zuciya, daga ƙarshe sai Sonali ta yi amfani da wani tsumma ta shaƙe mata wuya, daga nan rai ya yi halinsa.
Binciken da ƴan sanda suka gudanar ya nuna cewa marigayiyar ta koma zama a gidan ɗiyarta Sonali da mijinta, waɗanda suke zama tare da uwar mijin.
Sai dai bayanai sun ce tun bayan da ta koma gidan da zama take samu rashin jituwa da uwar mijin ɗiyar tata.
Lamarin ya yi ƙamari, inda a ranar Lahadi, toshuwa Biva cikin fushi ta buƙaci ɗiyar tata da ta kashe ta.
Yanzu dai ƴansanda suna tsare da Sonali bisa tuhumar ta da laifin kisan kai, bayan da ta ce ta kashe mahaifiyar tata ce domin cika umarnin da ta ba ta.













































