Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda na shiyya ta 13, Abayomi Oladipo, ya gargadi jami’an ‘yan sanda da su guji sanya abin rufe fuska ta yayin gudanar da ayyukansu.
Oladipo, wanda shiyya ta 13 ta kunshi jihohin Anambra da Enugu, ya yi wannan gargadi ne a ranar Larabar da ta gabata a Enugu yayin da yake jawabi ga manyan jami’an ‘yan sanda a ziyarar aiki ta yini daya da ya kai jihar.
Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sandan, ya ce, abubuwan da jsmi’sn ke yin amfani da su wajen rufe fuskar ba sa cikin kakin ‘yan sanda, inda ya kara da cewa ko kadan bai kamata wani babba ko jami’in da ke sa ido ya bar duk wadanda ke karkashin su yin kayan da ba su dace ba.
Ya kuma bukaci jami’ain da su rika kawar da duk wasu kayan da ska girke a shingayen gudanar da bincike.
Oladipo ya lura cewa barin yin amfani da irin wannan kayayyaki na iya haifar da hadurra da daddare ko kuma masu aikata laifuka su rika yin irin shingayen tare da nuna cewa su ‘yan sanda ne.
A cewarsa, dole jami’an su kasance a shirye a ofisoshinsu kuma su yi taka-tsan-tsan game da kewayen su saboda akwai yiwuwar a kai musu hari; Iyalai da masoyanku da rundunar ‘yan sandan Najeriya na bukatar ku da rai.
Dangane da walwala, Oladipo ya bukaci dukkan ma’aikatan da su tabbatar da cewa an cike bayanansu kuma an tabbatar da su yadda ya kamata, ya kara da cewa ya kamata a warware batutuwan dangi kuma dukkan ma’aikata su bayyana a fili.
Haka kuma Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sandan ya yaba wa kwamishinan ‘yan sandan jihar Enugu, Mamman Giwa, da rundunar ‘yan sandan bisa jajircewa da himma wajen ganin jihar ta kasance cikin kwanciyar hankali da tsaro ga mazauna cikinta har ma da masu zuba jari.
A nasa jawabin tun da farko, kwamishinan jihar ya ce, manyan kalubalen da rundunar ke fuskanta sun hada da rashin isassun ma’aikata da karancin kayan aiki.
Ya kara da cewa, duk da kokarin da ake yi na samar da dawwamammen zaman lafiya da tsaro a jihar, har yanzu akwai kalubalen rikicin manoma da makiyaya sai hare-haren kungiyoyin sa kai da ayyukan miyagun laifuka da dai sauransu.












































