An samu tashin hankali a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar Lahadi, bayan da ‘yan uwa mata biyu suka yi fada mai tsanani har ɗaya ta suma yayin da jami’an tsaro ke tambayarsu.
Lamarin ya faru ne bayan da suka rasa damar shiga jirgin United Airlines da suka saya tikitin tafiya, saboda sun iso filin jirgin bayan an rufe ƙofar shiga.
Wani ganau ya bayyana cewa suna cikin jirgi ɗaya, amma jinkirin da suka yi ya sa suka rasa damar hawa.
Daga nan ne suka fara fada yayin da ɗaya ke zargin ɗayar da ita ce ta jawo musu jinkiri.
Fadan ya fara da gardama, amma daga baya ya rikide zuwa duka da zagi a gaban sauran fasinjoji.
Fadan ya kawo cikas ga harkokin tafiya a wurin na wasu mintuna kafin jami’an tsaro su shawo kan lamarin.
Jami’an tsaron Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN) sashen Tsaron Jirgin Sama (AVSEC) ne suka shiga tsakani suka ja su zuwa ofishin bincike domin tambaya.
Sai dai yayin da ake tambayarsu, fadan ya sake barkewa a cikin ofishin, inda ɗaya daga cikin su ta fadi ƙasa ta suma.
Jami’an kiwon lafiya na FAAN suka kira motar asibiti domin kai ta asibiti, amma ‘yar uwarta ta ce matsalar ba ta likita ba ce, ta fi kama da ta Alhaji.
Duk da haka, ma’aikatan kiwon lafiya sun garzaya da ita asibitin FAAN da ke cikin filin jirgin.
Bisa bayanan da mai magana da yawun hukumar kula da harkokin sufurin Jiragen sama ta Ƙasa (NCAA), Mista Michael Achimugu, ya wallafa, ya ce an kai matakin gaggawa wajen taimakon matar da ta suma, kuma tana samun kulawa.
Har yanzu ba a tabbatar da cikakken halin da take ciki ba, yayin da hukumar kula da filayen Jiragen sama ta Ƙasa (FAAN) ba ta bayyana ko za ta ɗauki matakin ladabtarwa a kan su ba.
A cewar sashe na 19 na dokokin aiki na hukumar kula da sufurin Jiragen sama ta Ƙasa (NCAA), fasinjoji na da wajibin zuwa filin jirgi akalla awanni biyu kafin lokacin tashin jirgi domin kauce wa irin wannan matsala.













































