Masu kwacen waya sun kashe ɗalibin BUK a Kano

BUK 1 2
BUK 1 2

 

Wasu masu kwacen waya sun daba wa ɗalibin shekara ta uku na Jami’ar Bayero Kano (BUK), Umar Abdullahi Hafizi, wuka har lahira a unguwar Dorayi, ƙaramar hukumar Gwale a Kano.

Lamarin ya faru misalin ƙarfe 11 na dare, inda ya jefa al’ummar jami’ar cikin alhini da jimami.

Jami’ar ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga al’ummarta, inda ta tabbatar da cewa tana aiki tare da jami’an tsaro domin cafke masu laifin.

Shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya ce jami’ar na ƙoƙarin ganin an hukunta masu hannu a kisan.

Jami’ar ta yi kira ga ɗalibai da su kwantar da hankali tare da bada hadin kai wajen samar da bayanan da za su taimaka ga bincike.

A ƙarshe, BUK ta roƙi Allah ya jikansa, tare da baiwa iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here