Majalisar wakilan Najeriya ta cire kuɗi naira biliyan biyar da aka ware a cikin ƙaramin kasafin kuɗin ƙasar domin sayen jirgin ruwan shaƙatawa na shugaban ƙasa.
Shugaban kwamitin majalisar kan kasafin kuɗ, Abubakar Bichi ne ya sanar da hakan yau Alhamis bayan sun amince da ƙaramin kasafin kuɗin na naira tiriliyan 2.17.
Bichi ya shaida wa manema labaru cewa kwamitin ya mayar da kuɗn zuwa ɓangaren bashin karatu na gwamnatin tarayya, inda a yanzu kuɗin da aka ware wa bashin ya kai naira biliyan 10.
Dama dai batun sayen jirgin ruwan shaƙatawan na shugaban ƙasa ya haifar da muhawara a tsakanin al’umma, inda mutane da dama suka soki lamarin.