Majalisar Wakilai ta yi karatu na biyu ga kudurin tilastawa ƴan Najeriya kada kuri’a

Reps Speaker Abbass 720x430

Wani kudirin doka da ke ba da shawarar tilasta kada kuri’a a zaben ‘yan Najeriya da suka cancanta ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar wakilai.

Kudirin wanda kakakin majalisar Tajudeen Abbas ya dauki nauyinsa ya tsallake karatu na biyu ne bayan wata muhawara da aka tafka mai a ranar Alhamis.

Da yake jagorantar muhawarar, Daniel Ago, wanda ya dauki nauyin wannan doka, ya ce dokar da aka gabatar na neman yin kwaskwarima ga dokar zabe ta 2022 don magance matsalar karancin fitowar masu kada kuri’a.

Karin karatu: Ƴan majalisar wakilai 2 daga Kano sun fice daga jam’iyyar NNPP zuwa APC saboda rikicin cikin gida

Ya ce dokar kada kuri’a ta tilas za ta kara hada kai da jama’a da karuwar masu kada kuri’a, tare da sanya shigar zabe ya zama wajibi a shari’a maimakon zabi na kashin kai.

Ago ya ce kudirin, idan har ya zama doka, zai karfafa dimokuradiyya ta hanyar inganta wakilci, da samar da kasa mai sanin ya kamata, da kuma rage sayen kuri’u.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here