Kwamitin majakisar wakilan Najeriya da ke kula da harkokin sadarwa ya roki shugabannin kungiyar kwadago ta kasar ta NLC, da su fasa shiga yajin aikin kasa baki daya da suka shirya yi daga ranar Talata 4 ga watan nan nan Fabarairu 2025 saboda karin kashi 50 cikin dari na kudin kiran waya da intanet.
A kwanan nan ne hukumar sadarwa ta kasar ta amince da bukatar kamfanonin sadarwa ta kara kudin sadarwa da kashi 50 cikin dari saboda dalilai na karuwar kudin gudanar da harkokin kamfanonin.
Dangane da karin ne kungiyar ta NLC ta lashi takobin shiga yajin aikin kassa baki daya, tana mai kira ga gwamnatin tarayya da majalisun dokoki na tarayya su koma ga tsohon farashin.
Karanta har wa yau: “Ba za mu biya albashin da NLC ke so ba” —Tinubu
Kungiyar ta ce yajin aikin zai zama gargadi ga gwamnati kan hadarin irin wannan karin a kan al’ummar da ke fama da tsadar rayuwa – wadda mafi kankantar albashinta shi ne naira 70,000.
Baya ga karin kudin fetur da abinci da wutar lantarki da kuma sauran wahalhalu da al’ummar ke fama da su, in ji kungiyar kwadagon.