Majalisar wakilan tarayya ta fara shirin dakatar da aiwatar da tsarin gudanar da jarabawar WAEC ta 2026 ta hanyar amfani da na’ura mai ƙwaƙwalwa, wanda ma’aikatar ilimi ta tarayya ke shirin ƙaddamarwa.
Wannan mataki ya biyo bayan kudurin da dan majalisa Kelechi Nwogu daga jihar Rivers ya gabatar a zaman majalisar na ranar Alhamis, inda ya bukaci a jinkirta shirin saboda matsalolin da ke tattare da tsarin.
Dan majalisar ya bayyana cewa jarabawar WAEC ta shekarar 2025 ta gamu da tsaiko sakamakon matsalolin fasaha da suka hana ɗalibai samun sakamakonsu a kan lokaci, kuma hakan na iya sake faruwa idan aka gaggauta fara amfani da tsarin na kwamfuta a 2026.
Ya kuma bayyana cewa yawancin makarantu musamman a yankunan karkara ba su da kayan aikin kwamfuta, wutar lantarki mai ɗorewa da wadataccen internet, wanda hakan zai hana ɗalibai damar shiga jarabawar cikin adalci.
Majalisar ta bukaci a jinkirta aiwatar da tsarin zuwa tsakanin shekarun 2029 zuwa 2030 domin bayar da damar shirye-shirye da samar da kayan aiki a makarantu.
Ta kuma umarci ma’aikatar ilimi ta tarayya da ta jihohi su l samar da malamai da kayan fasaha a cikin kasafin kuɗi na gaba.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa majalisar ta kafa kwamiti na musamman don duba batun, tare da samar da cikakken rahoto kan yadda za a tabbatar da tsarin jarabawar kwamfuta mai inganci kafin aiwatarwa.













































