Majalisar wakilai ta kasa ta cimma matsayar dakatar da ƙarin kuɗin da ake caji na cire kuɗi a na’urar ATM da kuma soke batun cire kuɗi kyauta daga ATM ɗin da ba na bankin mutum ba, wanda Babban bankin Najeriya CBN ya yi.
Ƙudirin wanda ɗan majalisa Marcus Onubun ya gabatar, ya janyo hankalin majalisar kan sanarwar CBN game da ƙarin.
Ƴan majalisar sun nuna damuwarsu kan yadda wannan ƙari zai ƙara takura wa tattalin arziƙin ƴan ƙasar.
Karanta: Gwamnan Kano ya aike da suna daya zuwa majalisar dokoki domin tantance shi a matsayin kwamishina
Majalisar ta buƙaci CBN ya dakatar da tsarin gabanin yin tattaunawar da ta dace da kwamitocin kula da ayyukan bankuna da hada-hadar kuɗi da kuma cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe.
Tun a ranar 10 ga watan Fabrairun 2025 ne babban bankin ya sanar da cewa za a fara cazar kuɗi a duk lokacin da abokan hulɗar bankuna suka cire kuɗi daga na’urar ATM ɗin da ba ta bankinsu ba, kuma bankin ya ce za a fara aiwatar da hakan ne daga ranar 1 ga watan Maris, 2025.
Wannan lamari ya janyo ce-ce-kuce a tsakanin ƴan ƙasar da ke fama da mastin tattalin arziƙi da kuma tashin farashin kayan masarufi.