Majalisar wakilai ta goyi bayan ayyana dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a jihar Rivers mai fama da rikicin siyasa.
A ranar Talata ne Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Rivers tare da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Ngozi Odu da ƴan majalisar dokokin jihar Rivers tsawon wata shida sakamakon rikicin da jihar ta faɗa.
Kwana biyu bayan ɗaukan matakin ne Tinubu ya aike da takarda zuwa ga majalisar dokoki inda yake neman amincewarsu ga matakin da ya ɗauka.
Labari mai alaƙa: Majalisar Dattawa ta amince da dokar ta-bacin da Tinubu ya sanya a Rivers
A zaman da majalisar wakilai ta yi a dazun nan, kakakin majalisar wakilan, Tajuddeen Abbas ya karanto wasiƙar da Tinubu ya aike masu.
Ƴanmajalisar sun amince, da gagarumin rinjaye, matakin Tinubu na ayyana dokar ta-ɓacin.
A cewar kakakin majalisar, ƴanmajalisa 240 ne suka halarci zaman, hakan na nufin an samu adadin ƴanmajalisar da ake buƙata wajen amincewa da duka wani ƙudiri.
Matakin shugaba Tinubu dai ya yamutsa hazo a Najeriya inda al’ummar ƙasar ke tsokaci game da hurumi ko rashin hurumin shugaban ƙasar ya ɗauki irin wannan matsaya.
Ko a baya-bayan nan, wasu manyan ƴanadawa a Najeriya sun soki matakin da suka kira saɓa kundin tsarin mulkin ƙasar tare kuma da kira ga majalisar dokokin ƙasar da ta yi watsi da ƙudirin.