Kwamitin majalisar wakilan Najeriya kan karɓar ƙorafe-ƙorafen jama’a ya gayyaci babban kwanturolun hukumar kwastom na ƙasa, Adewale Adeniyi domin ya yi mata bayani kan abin da ya sa wasu manyan jami’an hukumar suka ƙi yin ritaya duk kuwa da lokacinsu ya yi.
Cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai na kwamitin, Chooks Oko ya fitar, ya ce an gayyaci babban jami’in hukumar ne domin ya yi bayani kan ƙorafin da aka shigar wa kwamitin dangane da ƙin yin ritaya da wasu manyan jami’an hukumar suka yi bayan lokacinsu ya yi.
Gidauniyar Obasi-Pherson Help ce ta shigar da ƙorafin gaban kwamitin, inda ta yi zargin cewa wasu jami’an hukumar masu muƙamin mataimakin kwanturola da masu muƙamin kwanturola sun ƙi ajiye aikinsu, bayan cikar lokacin.
karin karatu: Ƙudirin haraji ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai
Yayin bayar da sammacin, majalisar wakilan ta ce babban kwanturolan ƙasar ne kaɗai ke da haƙƙin bayyana wa ‘yan ƙasa ainihin gaskiyar wannan zargi.
“Ƴan Najeriya sun cancanci sanin gaskiyar abin da ya faru daga bakin babban konturolan…, a wannan lokaci da mafi yawan matasanmu ke neman ayyukan yi, indai batun nan gaskiya ne, to babu adalci ace ga wasu tsofaffin da suka isa ritaya su ƙi yin hakan,” a cewar shugaban kwamitin, Mike Etaba.
Ya ƙara da cewa ”ba wai muna ɗaukar ɓangare ba ne, muna nazarin kowane batu ne bisa gaskiya domin tabbatar da adalci ga waɗanda suka cancance shi”.